3 Yuli 2025 - 14:25
Source: ABNA24
Kanar Al-Watiri: Daruruwan Shugabannin Isra'ila Ne Aka Kashe A Harin Iran Kan Isra'ila + Bidiyo

Kanar Rashad Al-Watiri, wani sojan kasar Yemen kuma kwararre kan dabarun soji, ya shaidawa gidan talabijin na Channel 3 cewa: Idan da yakin ya dauki kwanaki 30, da an shafe Isra'ila gaba ɗaya.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) -Abna- ya habarta cewa: Iran ta yi amfani da kashi daya ne kacal na karfinta a yakin da take yi da Isra'ila.

Haifa ta zama garin fatalwa yayin da mutanen Iran suke cikin murna.

Wannan yaƙi ya bar gadon wutar hargitsi da rashin zaman lafiya a Isra'ila 

Bayan tuhumar Netanyahu da gazawa wajen shawo kan rikicin siyasa, tarzomar da magoya bayan tsohon firaministan suka yi ya tilasta dakatar da taron kotun kolin ƙasar.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun tabbatar da cewa yanayin da ake ciki a kasar ya yi tsamari sosai, har wasu suka yi kira da a aiwatar da hukuncin kisa kan babban alkalin kotun kolin ƙasar lamarin da manazarta ke ganin ya samo asali ne na tsawon shekaru da aka shafe ana aiwatar da manufofin raba kan jama'a da kuma yadda Netanyahu ya kaurace wa gamsar da jama'a.

A yau, Isra'ila ta fi kowane lokaci shiga cikin mummunan yanayin da Netanyahu ya jefa ta tare da rushewar cibiyoyin shari'a.

Your Comment

You are replying to: .
captcha